Shugabannin bankuna a Afrika sun yi kira ga gwamnatocin kasashe da su mayar da martani kan kalubalolin ababen more rayuwa dake hana ruwa gudu ga dunkulewar shiyyar, musamman ma sake tsare tsaren ayyukan ababen more rayuwa domin janyo hankalin masu zuba jari.
Da yake magana a yayin wani dandalin kasa da kasa kan zuba jari a Afrika da aka kammala a ranar Talata a Kigali, masu bankuna sun yi kashedin cewa, alfanun dunkulewar shiyyar ba zai cike ba yadda ya kamata idan babu gine ginen da suka dace.
Jonathan Magu, daretan zuba jari a bangaren makamashi da gine gine a gabashin Afrika a cikin Standard Bank, ya jaddada cewa zuba kudi a cikin gine gine na samun tsaiko dalilin babban hadari dake nasaba da ayyukan gine gine.
A halin yanzu gwamnati tana kashe kashi 10 cikin 100 na GDP dinta kan ababen more rayuwa kuma wani muhimmin kaso na bangaren wadannan kudade ana kebe shi kan sufuri, har ma da hanyoyin mota.
Mista Muga ya ce, game da jarin masu zaman kansu ta fuskar gine gine, an lura yawanci cewa, akwai gibi sosai tsakanin sakamakon da aka jira da gaskiyar halin da aka ciki. Don haka, yana da kyau da gwamnatoci su tsara tsarin yawancin ayyuka dake bukatar zuba kudin bangaren masu zaman kansu.
A nasa bangare George Negatu, darektan shiyyar gabashin Afrika a cikin bankin cigaban Afrika (BAD), ya bayyana cewa gamayyar kasashen gabashin Afrika na kasancewa wacce tafi dunkulewa da kyau a nahiyar, amma kuma rashin ingancin layukan sadarwa, karancin samun makamashi, da kuma karancin sufurin jiragen sama, jiragen kasa da kuma hanyoyin mota suna kawo jinkiri ga yin takara. (Maman Ada)