in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kara wasu sabbin yankunan musanya cikin 'yanci guda bakwai
2016-09-01 10:40:17 cri
Hukumomin kasar Sin sun dauki niyyar kafa wasu sabbin yankunan musanya cikin 'yanci guda bakwai (ZLE) a cikin kasar, wanda baki daya yawansu yake guda goma sha daya, a lokacin da kuma kasar Sin take hangen sake fadada nasarorin da ta samu na gwaje gwajen baya.

Sabbin ZLE za su kasance bi da bi a lardunan Liaoning, Zhejiang, Hunan, Hubei, Sichuan, Shaanxi, da kuma birnin Chongqing.

Wannan aikin fadadawa ya biyo bayan shekaru uku da kaddamar da ZLE na farko na kasar a Shanghai, domin gwajin wasu jerin sauye sauyen tattalin arzki, da ya hada da bude kofa ga masu zuba yarin waje da kuma rage wasu dokoki game da kwarar zuba jari.

Tare da karin wadannan yankunan musanya cikin 'yanci guda bakwai, kasar Sin na fatan ci gaba da kawo manyan manyan sauye sauye, duk da baiwa wadannan yankunan kasar damar amfana da matsayin da suke da shi bisa fasalin kasa da na masana'antu na musamman domin wasu sauran hanyoyin samun ci gaba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China