in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU na shirye-shiryen zaben shugabannin hukumar zartaswa
2016-08-11 09:27:38 cri

Kungiyar hadin kan kasashen Afirka ta AU, ta kaddamar da bude damar shiga takarar manyan mukaman shugabancin hukumar zartaswar ta 10, wadanda suka kunshi kujerar shugaba, da mataimaki, da kuma kwamishinonin kungiyar 8.

Wata sanarwa da sakatariyar kungiyar ta fitar jiya Laraba 10 ga wata, ta ce, an sanar da daukacin kasashe mambobin kungiyar jadawalin zaben, da kuma damar mika 'yan takara kafin cikar wa'adin da aka gindaya.

Ana dai fatan gudanar da zaben jagororin hukumar zartaswar kungiyar ta AU ne, a yayin taron shugabannin kasashe mambobinta na 28, wanda za a gudanar tsakanin ranekun 30 zuwa 31 ga watan Janairun shekara mai zuwa, a hedkwatar kungiyar dake birnin Addis Ababa, hedkwatar kasar Habasha.

Sanarwar ta kara wa cewa, ba a kai ga cimma nasarar zaben jagororin hukumar ba, a yayin taron da ya gudana a birnin Kigalin kasar Rwanda, kasancewar babu dan takara guda da ya samu kaso biyu bisa uku, na daukacin kuri'un da aka kada a zagaye 7 na zaben. Bisa tsarin zaben mai zuwa, tsoffin 'yan takara, da kuma sababbi na da ikon neman kujerun 10 da za a fafata zabe a kan su. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China