in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi maraba da sanya hannu kan jadawalin zaman lafiya a Sudan
2016-08-11 10:51:25 cri

Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta yi maraba da rattaba hannu tsakanin kungiyoyin adawa kan takardar zaman lafiya a kasar Sudan, tare da kimanta hakan a matsayin wani muhimmin cigaba da aka samu da zai taimaka wajen kawo karshen yake yake mai dorewa a cikin wannan kasa.

Kungiyoyin adawan sun rattaba hannu kan shawarar yarjejeniyar jadawalin da kungiyar AU ta gabatar a farkon wannan mako a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Shugabar kwamitin tarayyar Afrika AU, madam Nkosazama Dlamini-Zuma, ta yi marana da sanya hannun kan jadawalin aikin da aka tsara a cikin watan Maris din shekarar 2016 a karkashin wani kwamitin aiwatar na manyan jami'an AU kan kasar Sudan (AUHIP), in ji kungiyar AU a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.

Madam Dlamini-Zuma ta sake jaddada muhimmancin tattaunawa a matsayin wani shirin da zai kai ga amincewa ga wani sabon kundin tsarin mulkin kasa, da zai taimaka wajen fuskantar yawan kalubalolin da kasar Sudan take fama da su, da kuma zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da cigaba mai dorewa a Sudan, a cewar wannan sanarwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China