Babban sufeton AMISOM, John Marete, ya bayyana a yayin wani zaman taron fadakarwa na gamayyar kan yaki da kaifin kishin addini a Beletweyne cewa ta'addanci ita ce babbar barazana ga kokarin gwamnatin Somaliya ta fuskar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, haka kuma kare al'umommin shi ne babban nauyi na hukumomin tsaro da kuma jama'a.
Taron da 'yan sandan AMISOM suka shirya a ranar Laraba, na daga cikin jerin tarukan dake shafar fadakar da jama'a kan muhimmancin yaki da kaifin kishin addini kafin shirye shiryen zabuka masu zuwa, da zasu fara a cikin wannan watan.
Wakilan ma'aikatun gwamnati, matasa, mata da kungiyoyin fararen hula sun halarci wannan taro. Wasu kuma tarukan irin makamantan wannan zasu gudana a sauran biranen kasar.
Mataimakiyar kwamishinan 'yan sandan AMISOM, Cecilia Appiah Ampofo, ta bayyana cewa wannan taron zai baiwa matasa wata fahimta mai kyau kan mammunan tasirin kaifin kishin addini. (Maman Ada)