in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin tsaron Afrika na fatan ganin kawo karshen yake yake a Afrika
2016-08-05 10:27:20 cri
Shugabannin tsaron Afrika dake taro a Kigali na kasar Rwanda sun yi kira a ranar Alhamis da a dauki matakai masu karfi da kuma matakan siyasa na kawo sauyi domin kawo karshen yake yake dake daidaita nahiyar Afrika.

Sun yi wannan kira a yayin bikin bude taron kwamitin harkokin leken asiri da ayyukan tsaron Afrika (CISSA).

Taron ya tattara shugabannin hukumomin leken asiri na kasashen Afrika 51 da kuma kwararru a fannin tsaro domin yin nazari sosai kan hanyoyin da kasashen Afrika za su bi domin kawar da bazaranar tsaro dake bazuwa a halin yanzu a dukkan nahiyar.

Rashin dorewar siyasa da manyan laifuffukan kasa da kasa sun kasance babbar barazana sosai ga ci gaban tattalin arziki da al'umma a Afrika. Wata mafitar siyasar gaske ta kasance wajibi domin kawo karshen rikice rikice masu sarkakiya dake janyo bala'i ga nahiyar Afrika, in ji Juan Antonio Bibang Nchuchuma, shugaban CISSA.

Haka kuma, ya yi kira ga dukkan jami'an tsaron nahiyar da su taka muhimmiyar rawa da daukar matakin gaske domin hana jin karar makamai a Afrika.

"Burinmu shi ne na ganin an raba Afrika da yake yake nan da shekarar 2020. Za a iyar tabbatar da wannan burin ta hanyar kafa wasu nagartattun tsare tsare da karfafa dangantaka wajen yaki da kungiyoyi masu makamai da ta'addanci daga dukkan nau'o'insa", in ji mista Nchuchuma.

A halin yazu kasashen Afrika na fama da tashe-tashen hankali da yake yake. RDC-Congo, Burundi, Afrika ta Tsakiya da Sudan ta Kudu suna kasancewa cikin hadari, dalilin sake bullowar yake yake, in ji jami'in.

A nasa bangare, mista Erastus Mwencha, mataimakin shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afrika (AU), ya bayyana cewa wannan zaman taro zai taka muhimmiyar rawa domin dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar Afrika. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China