in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya bayyana matsayin Sin a yayin taron IAEA
2016-09-27 10:52:35 cri

A jiya Litinin ne aka bude babban taron hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA karo na 60 a birnin Vienna, inda shugaban tawagar wakilan Sin kuma mataimakin darektan hukumar makamashin nukiliya ta kasar Sin Wang Yiren ya bayyana matsayin kasar Sin kan aikin raya makamashin nukiliya.

Mr. Wang Yiren ya ce, tsaron nukiliya shi ne tushen raya makamashin nukiliya, kuma kasar Sin ta dora muhimmanci matuka kan tabbatar da tsaro da inganci a yayin raya makamashin nukiliya, ta bullo da tsarin sa ido kan tsaron nukiliya mai inganci, da kuma tabbatar da tsaron makamashin nukiliya yadda ya kamata.

Mr. Wang ya kara da cewa, tun lokacin da aka kafa hukumar IAEA a shekarar 1957, hukumar take martaba ka'idojin da hukumar IAEA ta kindaya yadda ya kamata. Haka kuma ta ba da gudummawa sosai wajen yin amfani da makamashin nukiliya cikin ruwan sanyi da hana karuwar makaman nukiliya a duniya, a kokarin samun zaman lafiya, wadata, da ci gaba mai dorewa a duniya.

Babban darektan hukumar IAEA Yukiya Amano ya bayyana a yayin bikin bude taron cewa, yin amfani da makamashin nukiliya cikin lumana zai rage yawan iska mai dumamma yanayi da ake fitarwa. A cewarsa, nahiyar Asiya, musamman ma kasar Sin, ta zama wurin da ya fi samun bunkasuwar makamashin nukiliya a duniya. Kana, ya jinjina gudummawar da kasar Sin take bayarwa wajen raya makamashin nukiliya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China