An zartas da kuduri a gun taron kwamitin musamman na wakilan hukumar IAEA a Litinin din da ta gabata, inda aka tsai da kudurin cewa, hukumar za ta kawo karshen bincike da ta shafe shekaru 12 tana gudanarwa kan kasar Iran game da batun kera makaman nukiliya a asirce.
Kudurin ya ce, bisa rahoton bincike na karshe da hukumar IAEA ta fitar, ya nuna cewar an kammala dukkan ayyukan tantance shirin nukiliya na Iran cikin lokaci, a sakamakon haka, kwamitin na musamman ya kawo karshen yin bincike kan wannan batu.
Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa a birnin Vienna Cheng Jingye, ya bayyana a gun taron cewa, wannan kuduri yana da matukar hangen nesa, ya dace da yarjejeniyar batun makaman nukiliya na Iran, kuma ya bayyana ra'ayoyin kasashe mambobin kungiyar. Ya yi imanin cewar, kudurin zai inganta ayyukan gudanar da cikkakiyar yarjejeniyar makaman nukiliya na Iran yadda ya kamata.
Mr. Cheng, ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan wannan kuduri zai kyautata huldar dake tsakanin hukumar IAEA da kasar Iran.
A nasa bangare, ministan harkokin waje na kasar Iran Mohammad Javad Zarif, ya bayyana a Litinin din nan cewar, kasar Iran tana maraba da wannan kuduri. Sannan kuma, kasar Iran za ta ci gaba da bin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya.(Lami)