Babban daraktan IAEA ya yaba matakan Sin na bunkasa samar da wutar lantarki ta hanyar makamashin nukiliya
Babban daraktan hukumar makamashin nukiliya ta duniya wato IAEA Yukiya Amano ya bayyana jiya a birnin Geneva cewa, a yanzu haka kasar Sin na bunkasa sabbin fasahohin samar da wutar lantarki ta hanyar makamashin nukiliya, tana kuma mayar da hankali kan tsaron nukiliya. Wadannan ayyukan da kasar Sin ke yi sun karfafa gwiwar kasashen duniya a wannan fannin.
Yukiya Amano ya bayyana haka ne bayan da ya ziyarci rumfunan kasar Sin, da aka baje kolin na'urorin "Hua Long1" dake amfani da sabuwar fasahar nukiliya,da na'urar PWR mai lamba "CAP1400" da kasar Sin ta kere da kanta
Yukiya Amano ya kara da cewa, yana da muhimmanci a habaka sabbin fasahohi da karfafa ingancinsu wajen tabbatar da makomar samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da karfin nukiliya. (Bilkisu)