Mataimakin wakilin kasar Sin a MDD Wang Min, ya yi kira ga hukumar kula da makamashin nukiya ta duniya IAEA, da ta kara kaimi wajen tabbatar da tsaron nukiliya yadda ya kamata.
Wang Min, wanda ya bayyana hakan yayin babban zaman majalissar kan wani rahoto da hukumar ta IAEA ta gabatar, ya ce, hukumar ta samu manyan nasarori a fagen tabbatar da amfani da makamashin nukiliyar ta hanyar lumana, da bunkasa fasahohi, tare da hana yaduwar makamai masu illa, da ma tsaron makamashin yadda ya dace.
Game da aiwatar da manufofin hadin gwiwa a fannin samar da makamashi, da fasahohin zamani kuwa, Mr. Wang ya ce, kamata ya yi a baiwa kasashe masu tasowa tallafin duk da ya dace, domin samun damar cin moriyar alfanun dake tattare da amfani da makamashin nukiliyar ta hanyoyin lumana.
Ya ce, kasar Sin na da burin ba da tata gudummawa, ciki hadda tallafin fasahohi, da kwarewa da ta samu a fannin amfani da makamashin na nukiliya a ayyukan fararen hula. (Saminu)