Mr.Yukiya Amano ya fada wa manema labaru cewa, game da zargin da aka yi wa Iran cewa, wai tana gudanar da shirin kera makamin nukiliya cikin siri, wannan batu ne mai sarkakiya, don haka, hukumar IAEA ba ta da tabbas a kai. Mambobin hukumar za su tsaida kuduri bisa wannan rahoto, ciki har da ko za a kawo karshen batun nukiliya na kasar Iran ko a'a a yayin taron majalisar zartaswar hukumar. (Bako)