Bisa yarjejeniyar nukiliya Iran da aka cimma a ranar 14 ga watan Yulin shekarar 2015, Iran ta amince rage shirinta na nukiliya bisa alkawarin janye wasu takunkumi da kasashen tarayyar Turai, Amurka da MDD suka sanya mata.
Mambobin kwamitin AIEA sun amince a cikin watan Disamban da ya gabata na ajiye batun shirin nukiliya na Iran, ganin cewa hukumomin Teheran sun yi hadin gwiwa tare da hukumar wajen warware wannan matsala.
Game da wannan batu, Sakatare-janar na MDD Ban Ki-moon ya nuna yabo a ranar Asabar kan aiwatar da wannan yarjejeniyar ta batun nukiliyan Iran, da ya kimanta da wani muhimmin mataki, a cikin wata sanarwa ta bakin kakakinsa.
Idan ya kuma fitata da nuna yabo game da nacewar bangarorin da abin ya shafa wajen tabbatar da sakamakon da aka samu.
Mista Ban ya nuna goyon baya ga bangarorin na su ci gaba da aiwatar da shirin aiki a cikin watanni da shekaru masu zuwa, a cewar wannan sanarwa.
Tare kuma da bayyana fatansa na ganin nasarar wannan yarjejeniya ta taimaka sosai ga dangantakar shiyya shiyya da kuma kasa da kasa wajen zaman lafiya, tsaro da zaman karko a shiyyar da duniya baki daya. (Maman Ada)