Kungiyar yawon bude ido ta duniya (OMT) ta jaddada niyyarta ta ci gaba da tallafa wa kasashen Afrika wajen kara yawan zuwan 'yan yawon bude ido a nahiyar domin ingiza bunkasuwar tattalin arziki da samar da guraben ayyukan yi a nahiyar. Elcia Grandcourt, darektar reshen Afrika na kungiyar OMT, ta bayyana a ranar jiya Jumma'a 16 ga wata a yayin wani taron kara wa juna sani na kwanaki uku dake gudana a birnin Addis-Abeba na kasar Habasha cewa, kungiyar ta OMT tana dukufa wajen taimaka wa kasashen Afrika wajen tinkarar kalubaloli a bangaren yawon bude ido, musammun ma wajen saukaka samun takardun visa, kyautata dokoki da raya ababen more rayuwar jama'a masu dacewa, da tsara manufa mai kyau. (Maman Ada)