A jawabinsa, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, yadda tattalin arzikin ke gudana, ya nuna a zahiri sabon tsarin yau da kullum na tattalin arzikin Sin, tilas ne a nuna imani a kokarin da ake yi na yin kwaskwarima kan tsarin samar da kayayyaki, da bullo da sabon tsarin tattalin arziki, da kuma karfafa bullo da matakan bunkasa tattalin arzikin kasar. (Zainab)