Lu Kang ya kara da cewa, yanzu tattalin arzikin kasar Sin na tafiya da kyau kamar yadda aka tsara. Dalilin bunkasar tattalin arzikin kasar Sin shi ne manufar nan ta yin gyare-gyare da nufin canja salon bunkasar tattalin arzikin, da sauya tsarin masana'antu a kokarin neman dawaumammen ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba.
Sannan Lu Kang ya ce, a cikin shirin shekaru biyar-biyar karo na 13 na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Sin, kasar Sin na kokarin neman ci gaba ta hanyar kirkiro sabbin fasahohin zamani, da neman daidaito tsakanin bangarori daban daban ba tare da gurbata muhalli ba, da ci gaba da bude kofa ga kasashen duniya domin kokarin more fasahohin neman samun ci gaba." Lu Kang ya tabbatar da cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai kara samun ci gaba cikin sauri, kuma za a samar wa sauran kasashen duniya karin damar neman ci gaba. (Sanusi Chen)