A yayin bikin, an kulla jerin yarjejeniyoyin hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da ciniki, wadda darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 18, wadanda kuma suka shafi sana'o'in kimiyya da fasaha da aikin gona da hada-hadar kudi da sauransu.
Wannan bikin baje koli na kasar Sin da nahiyoyin Turai da Asiya ya kafa sabon tarihi a fannonin da suka shafi fadin wuri da yawan kayayyaki da aka baje da kuma yawan kamfannoni mahalartan bikin. A yayin bikin, an yi nasarar kulla kwangiloli 200 tare da kamfanonin jihar Xinjiang, wadanda yawan kudaden ya kai kudin Sin Yuan biliyan 241.2. Kana jimillar kudin cinikin da za a yi tare da kasashen waje zai zarce dalar Amurka biliyan 4.9.(Lami)