in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron kara wa juna sani kan shirin ziri daya da hanya daya na shekarar 2016 a birnin Xi'an
2016-09-26 13:12:24 cri

An bude taron kara wa juna sani kan shirin ziri daya da hanya daya na shekarar 2016 a yau Litinin a birnin Xi'an, mamban ofishin siyasa na zaunannen kwamitin tsakiya na JKS, kuma ministan yada bayanai na Sin Liu Qibao ya halarci taron.

A cikin jawabinsa, Mr. Liu ya jaddada cewa, ya kamata a shimfida hanyoyin da za su hade kasashe daban daban, kana a kara fadada musayar ra'ayoyi a tsakanin jama'a, a yayin da ake gudanar da shirin ziri daya da hanya daya, domin kara fahimtar juna, da cimma daidaito a tsakanin al'ummomin da ke da al'adu da addinai daban daban na kasashen da shirin ya shafa. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China