in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin bom ya haddasa mutuwar mutum 1 a Mogadishu
2016-09-22 10:42:23 cri
'Yan sandan kasar Somaliya sun sanar da cewa, an kai harin bom a birnin Mogadishu, hedkwatar kasar Somaliya, a ranar Laraba, lamarin da ya haddasa mutuwar a kalla mutum 1, da raunatar wasu 3.

Bisa rahoton da 'yan sanda suka gabatar, an ce masu kai harin sun dasa wata nakiya a karkashin motar wani jami'in tsaro. Sa'an nan bayan da jami'in ya ta da mota, bom din ya fashe, wanda lamarin ya kashe jami'in nan take. Wasu jami'an tsaro 3 sun ji raunuka masu tsanani.

Har yanzu babu wanda ya dauki alhakin harin, sai dai ana tuhumar cewa kungiyar Al-Shabaab ce take da hannu cikin lamarin, ganin kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta dade tana kai irin wadannan hare-hare.

Za a gudanar da zaben majalisun kasar Somaliya a kwanaki masu zuwa, kuma kungiyar Al-Shabaab na kasancewa wata babbar barazana da kasar take fuskanta .(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China