in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojoji hudu sun mutu sakamakon harin da Al-Shabaab ta kai a Somaliya
2016-09-18 12:24:22 cri

Kakakin sojojin gwamnatin kasar Somaliya ya bayyana a jiya Asabar cewa, mayakan kungiya mai tsattsauran ra'ayi ta Al-Shabaab sun kai hari, inda suka kwace wani gari a yankin Gedo dake kudancin kasar a ran 16 ga wata, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojojin gwamnati a kalla 4, kana daya kuma ya ji rauni.

Kakakin sojojin gwamnati dake yankin Gedo Sheikh Aden ya ce, masu fafutukar na Al-Shabaab sun shafe sa'o'I da dama suna kai hari kan sansanin sojojin gwamnati dake wannan yankin. Koda ya ke sojojin gwamnati sun yi kokarin dakile maharan, amma a karshe masu mayakan suka kwace wannan gari. Amma duk da haka, kungiyar ta Al-Shabaab ta rasa wasu daga cikin mayakanta a wannan fafatawa.

Rahotanni na cewa, wannan gari dake yankin Gedo ya taba fadawa hannun Al-Shabaab, amma daga bisani sojojin gwamnatin Somaliya tare da taimakon sojojin kungiyar ta AU dake kasar suka sake kwace garin a shekarar 2011. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China