in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin gabashin Afrika sun kira da a gudanar da zabuka cikin 'yanci da adalci a Somaliya
2016-09-14 10:06:28 cri
Shugabannin kasashen gabashin Afrika sun kammala wani zaman taro na yini guda a ranar Talata da yamma a Mogadiscio, babban birnini Somaliya, tare da yin kira da a gudanar zabuka cikin 'yanci da adalci a yayin zabukan da aka tsaida shiryawa a karshen watan Satumba da Oktoba.

Shugabannin dake halarta wani dandalin musammun na kungiyar IGAD, tsakanin shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, shugaban Uganda Yoweri Museveni, faraministan Habasha Hailemariam Desalegn da shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud sun rattaba hannu kan wani jadawalin zabe na kasar Somaliya na shekarar 2016.

Shugabannin sun nuna kwarin gwiwa ga dukkan 'yan Somaliya da su halarci aikin zaben na shekarar 2016 tare da fatan ganin zabukan cikin 'yanci da adalci sun gudana cikin wadannan wa'adi, in ji shugabannin a cikin wata sanarwa a birnin Mogadiscio.

Haka kuma, sun nuna yabo ga niyyar gwamnatin tarayya ta Somaliya na tafiyar da wani tsarin zabe na sahihanci, na gaskiya da kuma kowa zai shiga da zai ga wani mulkin wucin gadi na zaman lafiya da demokuradiyya.

Gwamnatin tarayya ta aiwatar da zabuka ba na kai tsaye ba a Somaliya tare da fitar a cikin watan da ya gabata da wani jadawalin zabe na shekarar 2016.

Wannan jawadali na fayyace gudanar da zaben wata sabuwar majalisar tarayya a tsakanin ranar 24 ga watan Satumba da ranar 10 ga watan Oktoba, da kuma zaben shugaban kasa a ranar 30 ga watan Oktoba, ya samu amincewa daga dandalin jagoranci na kasar Somaliya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China