in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojojin Syria ta sanar da tsagaita wuta na kwanaki bakwai a dukkan fadin kasar
2016-09-13 12:09:25 cri
Rundunar sojojin kasar Syria ta sanar da wani shirin tsagaita wuta na kwanaki bakwai a dukkan fadin kasar tun daga ranar Litinin, in ji kamfanin dillancin labarai na SANA. Tsagaita wutar ya fara a ranar Litinin da misalin karfe bakwai na yamma bisa agogon wurin, kuma zai cigaba har zuwa ranar 19 ga watan Satumba, in ji rundunar sojojin Syria a cikin wata sanarwa. Sai dai, rundunar ta jaddada cewa tana da 'yancin mayar da martani da duk wani kuskuren take yarjejeniyar tsagaita wuta daga bangaren 'yan tawaye.

Sanarwar tsagaita wuta na cikin tsarin yarjejeniyar baya bayan nan da aka cimma tsakanin Amurka da Rasha. Kasashen biyu sun sanar a ranar Asabar da ta gabata cewa sun kai ga cimma wata muhimmiyar yarjejeniyar kan tsagaita wuta ta kasa a Syria, da zata fara aiki tare da fara sallar layya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China