in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tunisia ta sanar da sake bude ofishin jakadancinta dake Libya
2016-04-05 13:15:30 cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Tunisia ta bayar da wata sanarwa a ranar 4 ga wata cewa, za ta sake bude ofishin jakadancinta dake kasar Libya don nuna goyon baya ga gwamnatin hadin kan al'ummar kasar Libya da ta gudanar da harkokinta a birnin Tripoli.

Sanarwar ta bayyana cewa, ganin cewa gwamnatin hadin kan al'ummar kasar Libya ta koma birnin Tripoli, kasar Tunisia ta tsai da kudurin sake bude ofshin jakadancinta, da maido da harkokin diplomasiyya domin nuna goyon baya ga yunkurin kafa gwamnatin wucin gadi a kasar ta Libya.

A watan Agusta na shekarar 2014, dakarun Libya Dawn sun mamaye birnin Tripoli, gwamnatin kasar Libya da majalisar wakilan jama'ar kasar sun kaura zuwa birnin Tobruk dake gabashin kasar. Daga baya, dakarun Libya Dawn sun nuna goyon baya ga majalisar dokokin kasar da wa'adinta ya kare ta kasance gwamnatin taimakawa kasar. Lamarin da ya janyo kasancewar gwamnatoci biyu da majalisun dokoki biyu a lokaci guda a kasar Libya.

Don tabbatar da tsaronsu, kasashe da dama ciki har da kasar Tunisia sun rufe ofisoshin jakadancinsu dake Libya.

Bayan da MDD ta yi shiga-tsakani, wakilan majalisun dokokin biyu na kasar Libya sun daddale yarjejeniyar siyasa a watan Disamba na shekarar 2015, inda suka amince da kawo karshen baraka, tare da kafa gwamnatin hadin kan al'ummar kasar tare. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China