in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tunisia ta kara karfin tsaro a kasar
2015-12-19 13:24:41 cri

Ministan harkokin cikin gida na kasar Tunisia Mista Najem Gharsalli ya sanar a jiya Juma'a 18 ga wata cewa, kasar ta daga matsayin tsaronta don tinkarar kalubalen tsaro a karshen wannan shekara.

Najem Gharsalli ya kuma shedawa manema labaru cewa, za a kara karfin tsaro tun daga ranar litinin 21 ga watan, masu aikin tsaro za su kara karfin kai sintiri da ba da tsaro, don tabbatar da zaman lafiya a bukukuwan da za a gudana a karshen shekarar.

A cewarsa, halin tsaron da Tunisia ke ciki na samun kyautatuwa sosai, ma'aikatar tsaron kasar ta murkushe hare-haren da aka yi shirin kaiwa wuraren bude ido da wasu gine-ginen manyan hukumomi.

Idan ba a manta ba, an yi garkuwa da mutane a ranar 18 ga watan Maris a wani gidan ajiye abubuwan gargajiya dake birnin Tunisia hedkwatar kasar, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 23. A ranar 26 ga watan Yuni kuma, an kai hari kan wani Otel a birnin Sousse dake dab da teku, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 38. Haka kuma, a ranar 24 ga watan Nuwamba, an kai harin kunar bakin wake a birnin Tunisia, abin da ya sa mutane 13 sun rasa rayukansu. Dukkanin wadannan hare-hare uku, kungiyar tsattsauran ra'ayi na IS ne, ta sanar da dauki alhakin aiwatar da su. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China