in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 45 sun mutu a sakamakon farmakin da aka kai a wani kauye a kasar Congo
2016-08-15 11:14:52 cri

Wani jami'in gwamnatin kasar Congo Kinshasa ya furta a jiya Litinin cewa, dakarun adawa da gwamnatin kasar Uganda sun kai farmaki a wani kauyen dake gabashin kasar Congo Kinshasa a ranar 13 ga wata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 45.

Shugaban kasar Congo Kinshasa Josef Kabila ya zargi wannan farmaki da cewa farmakin ta'addanci ne. Ya kuma kara da cewa, "wannan farmakin kisan kiyashi ba shi da bambanci da ayyukan ta'addanci da suka faru a kasashen Mali da Faransa da Somaliya da kuma sauran kasashen duniya." Sannan ya yi kira ga kasashen duniya su dora muhimmanci kan ayyukan ta'addanci da suka faru a kasar Congo Kinshasa.

Tun daga shekarar bara, dakarun adawa na kasar Uganda sun hallaka duban mutane a jihar Kivu ta arewa maso gabashin kasar Congo. Sojojin kasar sun dauki matakan soja sau da dama domin yaki da wadannan dakaru.

Gabashin kasar Congo Kinshasa yana dab da kasar Uganda, inda a kan samu tashe-tashen hankula, dakarun adawa na kasar Uganda dake zaune a wurin su kan kai hare-hare tun kusan shekaru 20 da suka gabata.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China