in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
RDC: Jam'iyyar adawa ta UDPS ta ce matakin kotun kolin kasar ya sabawa kundin tsarin mulki
2016-05-17 10:38:12 cri
Jam'iyyar tabbatar da tsarin demokaradiya da ci gaban jama'a (UDPS), babbar jam'iyyar adawa a kasar RD-Congo, ta bayyana cewa matakin baya bayan nan da kotun kolin kasar ta dauka bisa yin amfani da kuduri mai lamba 70 na kundin tsarin mulki kan wa'adin shugaban kasa ya sabawa kundin tsarin mulki. A yayin wata ganawa tare da manema labarai a ranar Litinin a birnin Kinshasa, mataimakin sakatare-janar na UDPS, Bruno Tshibala, ya nuna cewa wannan kuduri ya karya lagon wadanda suke son halartar yin shawarwari. A cewar kudurin na kotun kolin RDC na ranar 11 ga watan Mayu, shugaba Joseph Kabila zai iya ci gaba da tsayawa kan mukaminsa bayan wa'adinsa, a karshen shekarar 2016, idan aka kasa shirya zaben shugaban kasa a wannan shekara. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China