Wakilin UNHCR dake kasar Sudan Mohamed Adar ya bayyana yayin da yake ganawa da jami'an ma'aikatar harkokin gida ta Sudan da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta kasar cewa, MDD za ta samar da gudummawar jin kai ga 'yan gudun hijira na kasar Syria fiye da dubu 80 dake kasar Sudan. Adar ya yaba wa gwamnatin kasar Sudan da tallafin ilmi da kiwon lafiya da aikin yi da ta samar wa 'yan gudun hijira na kasar Syria da ke zaune a kasar.
Sudan ita ce kasar da ta fi karbar 'yan gudun hijira na kasar Syria. 'Yan gudun hijira na kasar Syria da dama ne suke zaune a kasar ta Sudan wadda tattalin arziki da tsaronta ba su kai matsayin na kasashen Turai ba, amma duk da haka suna iya samun aikin a kasar Sudan.
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta kasar Sudan tana ganin cewa, mai yiwuwa yawan 'yan gudun hijira daga kasar Syria da za su zo kasar Sudan zai karu. (Zainab)