in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Al-Bashar na Sudan ya rushe jagorancin yankin Darfur
2016-09-23 09:41:51 cri
Shugaba Omar al-Bashir na Sudan, ya zartas da dokar rushe jagorancin yankin Dafur ko (DRA) a takaice. Kafofin yada labarun kasar sun bayyana cewa, wannan doka ta tanaji sauke daukacin mambobin majalissar zartaswar yankin, da ma na majalissar dokoki daga ayyukan su.

Hakan dai tamkar tabbatar da yarjejeniyar Darfur ce, wadda aka fi sani da (DDPD), yarjejeniyar da ta kawo karshen wa'adin aikin mahukuntan yankin na Dafur tun cikin watan Yunin da ya gabata, bayan da al'ummar yankin suka kada kuri'un amincewa da kasancewa bangare na babban yankin kasar, maimakon zama yanki mai cin gashin kai.

Yanzu haka dai makwanni biyu ke nan da gudanar da wasu shagulgula na musamman a kasar ta Sudan, biyowa bayan kammalar wa'adin ikon mahukuntan yankin na Dafur, bikin da ya gudana a El Fasher, fadar mulkin yankin arewacin Darfur.

An dai cimma yarjejeniyar Darfur ta wanzar da zaman lafiya a yankin ne ranar 14 ga watan Yunin shekarar 2011, tsakanin tsagin gwamnatin kasar da na masu adawa, wadda ke karkashin El Tijani El-Sisi. Sai dai kuma kawo yanzu wasu manyan kungiyoyin 'yan adawar yankin kamar "Justice and Equality Movement" da "Sudan Liberation movements" basu kai ga shiga yarjejeniyar ba tukuna.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China