A wata sanarwar da shugaban kungiyar Etienne Tshisekedi ya rattabawa hannu, gamayyar kungiyoyin ta kunshi jam'iyyun adawa na jamhuriyar demokuradiyyar Congo, sun ce sun ki amincewa da wasu batutuwa, ciki har da batun da Kodjo ya sanar na kafa kwamitin da zai jagoranci shirya tattaunawar sulhun.
AU ce ta nada Kodjo a matsayin jami'in da zai jagoranci kwamitin sulhu wanda ake sa ran zai fara zamansa a ranar 30 ga watan Yulin 2016. (Ahmad Fagam)