Somaliya ta kaddamar da wani shirin kasa na yaki da kaifin kishin addini
Shugaban kasar Somaliya Cheikh Mohamud ya kaddamar a ranar Litinin da wani shirin kasa domin yaki da kaifin kishin addini a wannan kasa dake kusurwar Afrika. Mista Mohamud ya bayyana cewa shirin kasar daga dukkan fannoni kan rigakafi da yaki da kaifin kishin addini na kasar Somaliya ya zo daidai da kiran da MDD ta yi zuwa ga kasashe mambobi domin bunkasa wani shirin kasa na yaki da kaifin kishin addini, wanda kuma yawancin 'yan Somaliya suke yin allawadai da tsattsauyin ra'ayin addini. Haka kuma, cewa shirin an bunkasa shi tare da tuntubar manyan jami'an gwamnati, tare da sanya hannun hukumomin yankunan kasar da kuma kungiyoyin fararen hulla. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku