in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin injiniya na MDD da AU sun fara wani taro a Mogadishu
2016-09-13 09:49:58 cri
A jiya ne sojojin injiniya daga MDD da kungiyar tarayyar Afirka(AU) suka fara wani taron karawa juna sani na kwanaki biyu a birnin Mogadishun kasar Somaliya, da nufin lalubo hanyoyin kara karfin yakar mayakan Al-Shabaab.

Haka kuma injiniyoyi daga tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afirka(AMISON), da Burtaniya,ofishin ba da tallafi na MDD da ke kasar Somaliya(UNSOS) suna kokarin fito da hanyoyin da za su ba da tasu gudummawar a fannin injiniya ga tawagar kungiyar da ke Somaliya.

A jawabinsa na bude taro, wakilin musamman na shugabar hukumar zartarwar kungiyar tarayyar Afirka da ke Somaliya, Jakada Francisco Caeto Madeira, ya yi kira da a yi wa ayyukan injiniya gyaran fuska ta yadda za su samar da goyon bayan da ya dace ga tawagar ta AMISON a yakin da ta ke yi da mayakan Al-Shabaab.

Bayanai na nuna cewa, rawar da sojojin injiniya za su taka, sun hada da tsara gine-gine, girka na'urori, kula da zirga-zirgar dakaru, tabbatar da tsaro, daura damara da sauran muhimman rawar da ake bukata su taka a fagen daga, da kuma musayar ra'ayoyi kan matakan inganta ayyukansu kamar yadda ya ke kunshe cikin sabbin dokokin gudanar da ayyukan AMISON da kuma tsarin tafiyar da ayyukan tawagar na 2017 da aka yiwa gyaran fuska.

Tawagar AMISON da gwamnatin tarayyar kasar Somaliya dai za su taka muhimmiyar rawa a zabukan da kasar ta ke shirin gudanarwa nan ba da dadewa ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China