in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta hada yaran da rikicin Boko Haram ya kora
2016-08-13 14:18:48 cri
Gwamnatin Najeriya ta bayyana a ranar Jumma'a cewa ta hada yara fiye da 200 tare da iyayensu da rikicin Boko Haram ya shafa.

Aikin hada wadannan yara tare da iyayensu ya gudana tare da taimakon kungiyar Red Cross (CICR) bisa tsarin shirin maido da 'yan uwantaka cikin iyalai, in ji Saad Bello, darekta janar na hukumar kula da agajin gaggawa ta NEMA, a birnin Yola, dake arewacin kasar. Wadannan yara masu shekaru biyar zuwa goma sha biyu da haifuwa, sun fito daga garuruwan Bama da Baga dake Borno.

Muna da har yanzu kimanin yara 165 da basu tare da rakiyar 'yan uwansu a cikin sansanoni hudu da shirin ya shafa a Adamawa, in ji mista Bello a gaban 'yan jarida. Wasu iyalai daga Bama sun ziyarci sansanonin 'yan gudun hijira na Yola inda suka gano diyansu, kamar yadda jami'in ya bayyana.

Bayan bincike mai zurfi na hukumomin da abin ya shafa, an mika wadannan yara ga iyayensu, in ji shugaban NEMA.

Tare da taimakon Red Cross, hukumar tana namijin kokari, ta hanyoyi daban daban, domin tantance iyayen sauran yaran da basu tare da rakiyar 'yan uwansu.

Kungiyar Boko Haram, dake neman shimfida dokar musulunci a arewacin Najeriya, ta janyo mutuwar mutane kusan dubu 200 tare da tilastawa mutane fiye da miliyan 2,6 barin muhallinsu tun daga shekarar 2009. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China