Jami'in kula da shirin sake tsugunar da mayakan Boko Haram da suka tuba, birgediya janar Bamidele Shaffa ne ya bayyana hakan ga taron manema labarai a garin Gombe. Yana mai cewa, nan ba da dadewa ba, 'yan Boko Haram din da suka tuba za su iso garin Gombe domin fara cin gajiyar wannan shiri, wanda zai fara aiki a sansanin sake tsugunar da tsoffin mayakan.
Ya ce, a lokacin da tsoffin mayakan na Boko Haram suke sansanin samun horon,za a koyar musu illar tsattsauran ra'ayi, matakin da zai taimaka musu sake komawa cikin al'ummominsu ba tare da wata matsala ba.
Shafa ya kuma bayyana cewa, kimanin hukumomin gwamnatin tarayyar Najeriya 14 ciki har da jami'an tsaro ne za su yi aiki a wannan sansani
A na saran horas da tsoffin mayakan na Boko Haram sana'o'I i a kalla 12 (Ibrahim)