in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kara samun tashe-tashen hankula a kasar Syria
2016-09-07 10:12:46 cri

Kwamitin bincike kan batun rikicin Syria na MDD ya gabatar da rahoto a jiya Talata a birnin Geneva, game da yanayin hakkin bil Adam cikin watanni 6 na farkon wannan shekara.

Rahoton ya bayyana cewa, bayan da aka kasa tabbatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka kulla a watan Faburairu na wannan shekara, an samu karun hare hare da aka kai kan fararen hula a kasar Syria, yawan mutanen da suka mutu da wadanda suka jikkata ya karu sosai, a cikin wannan hali, tabbatar da zaman lafiya a kasar ya zama burin da ba za a iya cimmawa ba.

Bugu da kari, rahoton ya yi kira ga bangarori daban daban da batun Syria ya shafa da kuma kungiyoyin kasa da kasa da su yi alkawari a fannin siyasa, domin kalubalantar jam'iyyu daban daban wajen farfado da yin shawarwari a tsakaninsu, domin cimma burin kawo karshen rikice-rikice da kuma laifuffukan karya doka, ta yadda za a rage yawan wahalhalun da jama'ar kasar Syria suke fama da su.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China