A cikin jawabin da ya gabatar a gun taron shugabannin kasashen Asiya da na Turai karo na 11, firaminista Li ya bayyana cewa, sa kaimi ga bunkasuwar nahiyoyin Asiya da Turai zai samar da ci gaba a tsakanin shiyyoyin. Makasudin shirin "Ziri daya da hanya daya" da Sin ta gabatar shi ne domin yin shawarwari da samun ci gaba da kuma moriyar juna, wanda ya sami amincewar kasashen duniya masu yawa. An fara samun sakamako, wanda ya sa kaimi ga samar da guraben ayyukan yi da ci gaban tattalin arziki a wuraren.
Darektan manufofin kungiyar masu ba da shawara ta kungiyar EU mai taken "Abokiyar Turai", Shada Islam ya bayyana cewa, shirin "Ziri daya da hanya daya" da Sin ta bullo da shi, zai samar da sabon zarafi ga hadin gwiwa tsakanin Asiya da Turai a nan gaba. A sa'i daya kuma, wannan shiri ya bayyana kwarin gwiwa da alkawarin Sin na zurfafa dangantaka tsakanin nahiyoyin biyu da sa kaimi ga inganta mu'amala tsakaninsu.
Mataimakin babban shugaban bankin Kasikorn na Thailand, Wichai Kinchong Choi ya bayyana cewa, yin mu'amala da juna zai taka muhimmiyar rawa ga musaya da bunkasuwar tattalin arziki da al'adu tsakanin Asiya da Turai cikin sauri a nan gaba. Shirin "Ziri daya da hanya daya" yana ba da taimako sosai wajen sa kaimi ga yin mu'amala tsakanin shiyyoyin da batun ya shafa. Wannan shiri ya hada da gabashin Asiya, da Turai, da tsakiyar Asiya da Turai, shi ya sa zai kyautata hanyar samar da kayayyaki a Asiya da Turai, da kara sa kaimi wajen samar da manyan ayyuka don amfanin jama'a da hadin gwiwa a fannin samar da makamashi tsakanin kasashen dake dab da wannan layi, ta yadda zai sa kaimi ga hadin gwiwa da samun moriyar juna domin samun ci gaba tare.(Fatima)