An dai gudanar da tattauanawa mai zurfi a zagayen farko na taron, game da halin da tattalin arzikin duniya ya tsinci kansa a halin yanzu da irin kalubalolin da suke addabar sa, da kuma ba da fifiko game da tsare tsaren da suka shafi tattalin arzikin, da yadda za'a aiwatar da shirin muradu shekara ta 2030, don habaka harkokin kasuwanci, da samar da sahihin yanayi ga tattalin arzikin duniya, da kuma aikin kwadago da dokokin kudi na kasa da kasa.
Mista Li ya ce, a halin da ake ciki yanzu, tattalin arzikin duniya yana tafiyar hawainiya kuma harkokin kasuwanci a duniya na ci gaba da fuskantar koma baya. Abu mafi muhimmanci shi ne, wannan taron tattaunawa da aka shirya ya zo ne a daidai lokacin da tattalin arzikin duniya ke cikin garari.
Kasancewar wannan shi ne karon farko da aka shirya tattaunawar tsakanin manyan jami'an kudi na kasa da kasa da gwamantin kasar Sin, taron ya ambato irin azamar da kasar Sin take da shi wajen ci gaba da tuntubar kasashen duniya. Taron ya bayyana kyakkyawar fata wajen bullo da dabarun da za su taimaka wajen ci gaban tattalin arzikin duniya da kuma yin aiki tare da juna da samun bunkasuwa ga harkokin kasuwanci da tattalin arzikin duniya. (Ahmad Fagam)