Shugaba Jacob Zuma na kasar ya yaba wa ofishin jakadancin kasar Sin da Sinawa mazauna kasar bisa ga dinbin taimakon da suka baiwa kasarsa a kokarin bunkasa harkokin ba da ilmi tun bayan da aka kawo karshen nuna bambancin launin fata a kasar.
Shugaba Zuba ya bayyana hakan ne a jiya Laraba, a lokacin da ya halarci bikin watan tunawa da Nelson Mandela da aka shirya a birnin Ekurhuleni da ke lardin Gauteng a kasar Afirka ta kudu.
Ranar 18 ga watan Yuli, ita ce ranar da aka kebe don tunawa da Nelson Mandela, yayin da kasar Afirka ta kudu, ta kebe watan Yuli a matsayin watan tunawa da Nelson Mandela. Shugaba Jacob Zuma da gwamna Markkula na lardin Gauteng, da ministan kula da samar da ilimi a matakin farko na kasar Afirka ta kudu da Mr. Tian Xuejun, jakadan kasar Sin dake kasar Afirka ta kudu sun halarci bikin ba da kyautar kayayyaki da aka shirya a wata makarantar firamare.
A yayin bikin, shugaba Zuma ya bayyana cewa, a sabuwar Afirka ta kudu wadda take da 'yanci da bin tsarin dimokuradiyya da aka kafa bayan da aka yi watsi da dokokin nuna bambancin launin fata, zaman rayuwar jama'a ta samu kyautatuwa sosai, marigayi Nelson Mandela ya kasance tamkar wani abin koyi da ke sa kaimi ga al'ummomin duk duniya. A jajibirin ranar tunawa da Nelson Mandela ta kasa ta kasa ta karo ta 7, gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta mika wa daliban makarantar firamare ta Malulana guda 800 kyautar kayayyakin da 'yan kasuwa Sinawa wadanda mazauna kasar Afirka ta kudu suka bayar. (Sanusi Chen)