Mai magana da hukumar tsaron Amurkar Mark Toner, ya fada a lokacin taron manema labaru cewar, idan Rashar ta yi amfani da sansanin sojin saman kasar Iran wajen kaddamar da hare haren, babu abin da matakin zai haifar sai kara dagula al'amurra a yankin Aleppo da kewaye, haka kuma lamarin zai cigaba da illata fareren hula ne.
A ranar Talata ne kasar Rasha ta sanar da cewar mayakanta dauke da boma bomai sun nufi sansanin sojin saman Iran domin ci gaba da kaddamar da hare hare ta sama kan mayakan 'yan ta'adda a Syria, a yunkurin da Rashar ke yi na yaki da ta'addanci a yankin gabas ta tsakiya da kuma karfafa dangantakar dake tsakaninta da Iran.
Toner, ya kara da cewar, Amurkar na ci gaba da tantancewa ko yunkurin da Rasha ke yi ya saba da yarjejeniyar MDD ta 2231, wanda ta haramta sayarwa ko shigar da jiragen yaki zuwa kasar Iran. (Ahmad Fagam)