A jiya Talata ne hukumar tsaron kasar Amurka, ta bayyana cewa, Rasha ta sanar mata aiwatar da wasu farmaki ta sama, kan kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi, wadanda jiragen ta na yaki suka kaddamar daga Iran.
Hukumar tsaron kasar Rasha kuma ta sanar a wannan rana cewa, jiragen saman ta na jefa boma-bomai, sun tashi a karon farko daga sansanin jiragen sama dake jihar Hamadan ta kasar Iran, inda suka kai hari kan kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi, ciki hadda IS dake kasar Sham, kafin daga bisani su koma sansanin su. (Amina)