Kamfanin dillancin labaran IS Amaq, ya rawaito cewar, an hallaka al-Adnani ne a lokacin da yake korarin nazartar yadda 'ya'yan kungiyar ta IS za su kubuta daga hare hare dakarun sojoji a yankin na Aleppo.
Sai dai IS ba ta fayyace hakikanin wajen da aka kashe kakakin nata a Aleppon ba.
Marigayi al-Adnani guda ne daga cikin manyan kwamandojin babban jagoran kungiyar IS Abu Bakr Al-Baghdadi.
An haifi al-Adnani a arewa maso yammacin lardin Idlib, kuma ya taba yin aiki da kungiyar al-Qaida a Iraq a shekarar 2003. (Ahmad Fagam)