Wannan kira na kunshe ne cikin wani sabon rahoto da kungiyar mai ragin inganta aikin gona a Afirka(AGRA) ta fitar yau Talata,tana mai cewa, kasashen da suka aiwatar da shirin bunkasa aikin gona a Afirka yadda ya kamata, sun samu amfani gona mai tarin yawa da samun karuwar alakaluman GDP, kana sun magance matsalar abinci mai gina jiki da suke fuskanta idan aka kwatanta da kasashen da ba su rugumi shirin ba.
Shugabar shirin na AGRA Agnes Kalibata ta bayyana a lokacin kaddamar da wannan rahoto da ya gudana a birnin Nairobin kasar Kenya cewa, a cikin shekaru goman da suka gabata, an samu ci gaba a bangaren aikin gona, lamarin da ya kasance wani mataki na samun ci gaban tattalin arziki mai dorewa wanda ya yi tasiri a dukkan bangarorin rayuwar al'umma, musamman talakawa a nahiyar Afirka.(Ibrahim)