Darakta Ning ya bayyana haka ne a yayin da yake halartar taron dandalin tattaunawa kan zuba jari a Afirka karo na biyu da aka shirya a birnin Guangzhou na kasar Sin. Ning ya ce, kasashen Sin da Afirka suna gudanar da hadin kai ta fuskar masana'antu bisa burin neman ci gaba tare, kana ana mayar da hankali kan raya muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a, da cin gajiyar albarkatu da makamashi ta hanyar zuba jari kai tsaye, da gudanar da kwangilar gine-gine, da hadin kan cinikayyar na'urori da fasahohi, da nufin taimakawa kasashen Afrika raya masana'antunsu, da birane da kuma harkokin sadarwa. (Bilkisu)