Wannan mutum, da aka tantance shi bisa sunan Mudasiru Jibrin, an kama shi a ranar 17 ga watan Juli a wani gidan yarin kungiyar Boko Haram da 'yan sanda na leken asiri suka gano a jihar Kano din.
Binciken farko ya nuna cewa mista Jibrin shi ne ya jagoranci wani barin wuta kan daliban wata makarantar sakandare dake birnin Potiskum dake jihar Yobe a arewa maso gabashin kasar da kusan shekaru uku da suka gabata, a cewar hukumomin tsaron kasa a cikin wata sanarwa.
Tare da cake da ya daga cikin shugabannin Boko Haram, 'yan sandan leken asirin sun taba cake a ranar 8 ga watan Juli wani mayakin Boko Haram da ya yi karin suna tare da wasu abokansa uku a lokacin da suka ida kammala ayyukansu domin kai hare hare cikin hadin gwiwa a wuraren dake suka zaba a jihar Kaduna, a cewar wannan sanarwa.
A cewar wasu alkaluma, dalilin rikicin Boko Haram, mutane kusan dubu 20 suka rasa rayukansu kana fiye da miliyan 2 da dubu 600 suka kaura daga muhallinsu tun daga shekarar 2009. (Maman Ada)