in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Burundi ta yi alkawarin bullo da shirin shigar da zabayan kasar cikin al'umma
2016-06-15 11:39:51 cri
Kasar Burundi na shirya cimma wani shirin shigar da zabayan kasar cikin al'umma musamman ma domin kawo karshen kisan gillar da ake masu, in ji ministan harkokin jama'a da 'yancin jama'a Martin Nivyabandi a ranar Talata a kwanan nan a birnin Bujunbura.

A cikin wata hira da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua, minsta Nivyabandi a dabra da bikin aka kebe a ranar kasa da kasa ta biyu ta fadakarwa kan cutar zabaya, ya bayyana cewa irin wannan shiri zai taimaka wajen gudanar da ayyukan da suka dace domin shigar da zabayan kasar cikin al'umma yadda ya kamata.

A tsawon watanni goma sha biyu na baya bayan nan, zabaya 23 aka kashe a kasar Burundi dalilin wasu ayyukan tsafe tsafe dake nuna cewa wasu sashen jikin zabaya na kawo sa'a ta fuskar samun kudi.

Watsi da yara zabaya da iyalansu suke yi dalilin wadannan tsafe tsafe na janyo yawanci bacewar iyalai idan aka yi la'akari da cewa macen auran da ta haifi zabaya mijinta zai sake ta, lamarin da zai tilasta mata kula da danta ita kadai, in ji ministan.

Mista Nivyabandi yayi amfani da wannan dama domin yin kira ga 'yan kasarsa dasu nuna halayya mai kyau da hakuri domin karfa zamantakewa mai kyau tsakanin al'ummomin kasar duk da bambance bambance tare da sanyawa a kai cewa zabaya mutane kamar su. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China