Lazare Makayat Safouesse, shugaban tawagar ta AU mai wakilan kasashe 15 don tabbatar da zaman lafiya, ya bayyana kyakkyawar fatar cewar za'a iya cimma nasarar warware rikicin kasar Burundin kamar yadda aka taba cimma wata yarjejeniya a shekarar 2000, wanda aka yiwa taken Arusha Agreement.
Safouesse, wanda kuma jakada ne na jamhuriya dimokaradiyyar Congo a kungiyar ta AU, ya tabbatar da hakan ne a lokacin da yake ganawa da shugaban majalisar dattawan kasar Burundin Reverien Ndikuriyo.
Mai Magana da yawun shugaban majalisar dattijan Burundin Anicet Niyongabo ya shedawa 'yan jaridu cewa, an bukaci 'yan tawagar da su nuna goyon baya ga tattaunawar sulhunta rikicin kasar ta Burundi da ke gudana.