in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin MDD sun zargi kasar Koriya ta arewa kan gwajin makamin nukiliya da ta sake yi
2016-09-10 12:29:14 cri
A ranar Jumma'a 9 ga wata, Mr. Ban Ki-moon, babban sakataren MDD da Mr. Mogens Lykketoft, shugaba mai ci na babban taron MDD bi da bi ne suka zargi kasar Koriya ta arewa da ta sake yin gwajin makamin nukiliya, sun kuma nemi kasar Koriya ta arewa da ta dakatar da shirin nukiliyarta ba tare da bata lokaci ba. Bugu da kari, kwamitin sulhu na MDD ya kuma fitar da wata sanarwa, inda ya yi tir kan gwajin makamin nukiliya da kasar Koriya ta arewa ta sake yi kwanan nan, ya kuma nuna cewa, wannan matakin da Koriya ta arewa ta dauka ya saba wa yarjejeniyoyin MDD da abin ya shafa.

A lokacin da yake ganawa da manema labaru wadanda suke aiki a hedkwatar MDD, Ban Ki-moon ya ce, kasar Koriya ta arewa ta dauki matakin gwajin makamin nukiliya, lamari ne da ya saba wa yarjejeniyoyin MDD sosai, kuma zai kawo illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da ake da su a yankin da kasar take ciki. Sannan ya nemi kasar Koriya ta arewa da ta bi bukatun gamayyar kasa da kasa, na canja hanyar da take bi domin kokarin cimma burin rashin kasancewar nukiliya a yankin Koriya.

A nasa bangaren, cikin sanarwar da ya fitar, Mr. Mogens Lykketoft ya ce, wannan mataki ne da bai kamata a dauka ba, kuma ba a iya amincewa da shi domin zai kawo barazana sosai ga kokarin kasashen duniya na shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk duniya baki daya. Ya kuma nemi kasar Koriya ta arewa da ta kawar da shirinta na kera makaman nukiliya da makamai masu linzami domin sauke nauyin da kasashen duniya suka dora mata.

Sannan a cikin sanarwar da aka fitar bayan da mambobin kwamitin sulhu na MDD suka tattauna kan lamarin a asirce cikin gaggawa, ana ganin cewa, a bayyane ne matakin gwajin makamin nukiliya da kasar Koriya ta arewa ta dauka ya saba wa yarjejeniyoyin kwamitin sulhu na MDD da abin ya shafa da ma ka'idodjin hana yaduwar nukiliya. Sanarwar ta nuna cewa, bisa alkawarin da kwamitin sulhu ya taba dauka, da illar da wannan gwajin makamin nukiliya ya yi, bisa kundin MDD, kwamitiin sulhu na MDD zai dauki matakan da suka wajaba, tare kuma da bullo da wani sabon kuduri kan lamarin. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China