Frank La Rue, mataimakin darekta janar na UNESCO, dake kula da sadarwa da watsa labarai, ya bayyana a ranar Jummu'a a birnin Arusha, a yayin wani taron karawa juna sani kan kare 'yan jarida, cewa hukumomin MDD da na kungiyar tarayyar Afrika (AU) sun shirya wata tattaunawa ta tsakanin shiyya domin fadakar da jama'a da kuma taimakawa wajen karfafa karfin masanan Afrika ta fuskar 'yancin fadin albarkacin baki da kuma tsaron 'yan jarida.
Kariya ta fuskar shari'a ta 'yan jarida a lokacin da suke gudanar da aikinsu shi ne matakin farko mafi muhimmanci domin 'yancin fadin albarkacin baki, in ji mista Frank La Rue.
Idan har 'yan jarida suna cikin hadarin cikin karo da bazarana, ko tsare su ba bisa ka'ida ba, ko ma a kashe su domin sun bayar da labari ga jama'a, 'yancin fadin albarkacin baki zai ragu, da kuma takaita karfin al'umma wajen yin zabin da zai kasu tudun mun tsira, in ji jami'in. (Maman Ada)