Wannan kungiya an dora mata nauyin bincike kan amsar da tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Sudan ta Kudu (MINUSS) za ta bayar game da tashen tashen hankalin da suka barke a cikin watan Julin da ya gabata.
Kungiyar da janar Patrick Cammaert yake jagoranta, za ta yi nazari kan rahotonnin da suka shafi haduran hare hare kan fararen hula da kuma batutuwan cin zarafin mata da fyade da suka faru a yankunan ba da kariya ga fararen hula na MDD dake Juba.
A cewar wata sanarwa ta MINUSS, kungiyar za ta tantance idan tagawar ta mayar da martani cikin lokaci kuma yadda ya kamata domin rigakafin wadannan hadura da kuma kare fararen hula bisa ga kayayyakin aiki da kuma karfinta a lokacin abkuwar tashe tashen hankalin.
Bisa dalilan kasancewar haduran, da zarge zarge masu tsanani da kuma sakamakon wucin gadi na MINUSS, sakatare janar na MDD ya dauki niyyar kaddamar da wani bincike na musamman mai zaman kansa domin tantance abubuwan da suka faru a yayin wadannan tashe tashen hankali da kuma kimanta amsa baki daya ta tawagar, in ji wannan sanarwa.
Kwamitin binciken na kunshe da kwararrun da suka samu horo na soja, 'yan sanda, shiri'a, 'yancin dan adam da cin zarafin mata, za su gabatar da rahotonninsu ga sakatare janar na MDD a cikin wani wa'adi na wata guda. (Maman Ada)