in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu ya kara jefa kuri'u da nufin zaben babban sakataren MDD
2016-09-10 12:57:15 cri
Jiya Jumma'a kwamitin sulhu na MDD ya kara jefa kuri'u kan 'yan takara guda 10 dake neman kujerar babban sakataren kungiyar.

Wannan ne zagaye na hudu da aka jefa kuri'u kan zaben babban sakatare na nan gaba. A madadin shugaban kwamitin sulhu na wannan wata, kuma wakilin dindindin na kasar New Zealand dake MDD Gerard Bohemen, wakilin dindindin na kasar Rasha dake MDD Vitaly Churkin ya bayar da sanarwa ta bakinsa ga manema labaru bayan jefa kuri'un, amma bai sanar da sakamakon ba kamar yadda aka yi a da.

Sai dai akwai wasu jami'an diplomasiyya dake fayyace cewa, tsohon babban kwamishinan MDD dake kula da harkokin 'yan gudun hijira Antonio Guterres yana matsayin gaba ga yawan kuri'un da ya samu a wannan karo.

Bisa ajandar da kwamitin sulhu ya bayar, za a kara jefa kuri'u a zagaye na 5 a ranar 26 ga wata, daga baya kuma a farkon mako na watan Oktoba za a jefa kuri'u zagaye na 6.

Bisa tsarin MDD, dole ne kwamitin sulhu ya gabatar da babban sakataren MDD tukuna, daga baya kuma sai babban taron MDD ya nada shi. A cikin kasashe mambobi 15 na kwamitin sulhu, idan 'dan takarar yana son lashe zabe, tilas ne ya samu goyon baya daga wajen dukkan zaunannen kasashen MDD guda biyar, da kuma kasashe ba na dindindin ba a kalla 4.

Babban satakaren MDD na yanzu Ban Ki-Moon zai gama wa'adin aikinsa a karshen shekarar da muke ciki. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China