in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana adawa da masu neman tsoma baki a harkokin yankin Taiwan daga kasashen waje
2016-09-14 15:48:20 cri
A kwanakin baya ne, jagorar yankin Taiwan ta ce, hukumar yankin na fatan kasar Amurka ta sayar mata da makamai. Game da lamarin, Mr. Ma Xiaoguang, kakakin hukumar kula da harkokin yankin Taiwan ta kasar Sin ya bayyana a yau a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa cewa, ba mu yarda wasu daga kasashen waje su tsoma mana baki a harkokin yankin Taiwan ba, har kullum matsayin da kasar Sin take dauka kan yankin Taiwan a bayyane ya ke kuma bai canja ba.

Wani dan jarida ya yi tambayi a yayin taron manema labarun cewa, a kwanan baya, jagoran hukumar yankin Taiwan ta bayyana cewa, hukumar Taiwan tana fatan karfafa dangantakar soja a tsakaninta da kasar Amurka, ko me kakakin zai ce game da wannan batu? Ma Xiaoguang ya nuna cewa, muna son gaya wa hukumar yankin Taiwan, cewa matakin da ya dace na tabbatar da zaman lafiya da kyakkyawar makomar Taiwan shi ne, komawa ga hanya madaidaiciya dake iya tabbatar da bunkasa dangantaka tsakanin gabobi biyu na teku Taiwan cikin lumana kadai. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China