Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ne ya bayyana hakan, yayin da yake mayar da marhani game da yiwuwar yankin na gabatar da takardarsa ta neman zama mambam MDD.
Lu Kang ya ce, sanin kowa ne cewa, MDD kungiya ce ta kasa da kasa, wadda take kunshe da kasashe masu 'yanci, kuma kasa mai 'yanci ne za ta nemi zama mambobin majalisar.
Mr Lu ya kuma bayyana cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya, kana Taiwan wani yanki ne na kasar Sin. A saboda haka, gwamnati da al'ummar kasar Sin baki daya, suna adawa da duk wani mataki na neman 'yancin yankin Taiwan.
Rahotanni na nuna cewa, a makon da ya gabata ne babban wakilin yankin Taiwan a MDD Tsai Ming Shian ya bukaci sabuwar jagorar yankin Tsai Ing-Wen, da ta rubutawa babban sakataren MDD Ban Ki-moon takardar neman 'yancin yankin.
Amma a amsar da ya bayar ranar Alhamis, jami'in da ke kula da harkokin kasashen waje da ke yankin Taiwan ya bayyana cewa, hukumar yankin Taiwan ba za ta aikata matakan neman shiga MDD ba. (Ibrahim Yaya)